Umar Tata Ya Rubuta 03 August, 2019 DA BA DON.......!



Da ba don kar ace Tata na neman aikin yi ba, da ba don kar ace Tata yana nufin yafi kowa ba, da ba don kar ace Tata ya fara takara ta 2023 ba, da nace HE Aminu Bello Masari ya kirkiro mani Ministry For Internal Security, Refugee Rehabilitation, Reconstruction & Integration ya bani dama da jagorancin tsaro a jihar Katsina da da yardar Allah sai na koma Batsari na tare da zama. Da sai nabi gari gari da gida gida kauyukan Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume da Jibia na nemi alfarma don kawo karshen wadannan kashe kashe a cikin jihar Katsina. Zan nemi alfarmar masu alfarma, zan nemi taimakon masu hakki a kan wannan matsala, zan nemi afuwar wadanda ke cikin fushi in nemi hakkin wadanda aka zalunta don kawo zaman lafia a jiha ta. Ba zan fito wannan yanki ba sai zubar da jini ya lafa da yardar Allah, sannan yan gudun hijira sun koma gidajen su. In zan sami wannan damar zan so ba don in nemi gindin zama ga gwamnati ko neman takara a gaba ba a a sai don ganin al'umma ta ta zauna lafia!

Ni da ke kai gudummuwa a Faskari da Sabuwa ga wadanda irin wannan bala'in ya shafa yau gashi abun ya shigo har cikin gida na Dutsinma. Shirun mu, mu masu alfarma, tayi yawa sannan wahalar marassa galihu sai kara assasa take. Wasu zasu ba wannan magana tawa fassara iri iri amman Allah yasan babu komai a zuciyata illa ci gaban jiha ta da zaman lafiar al'umma ta. Muna da alfarma a ko ina a cikin jiha kuma in muka nema ana yi mamu to lokaci yayi da zamu neme ta ba a kan kuri'a ba!

Comments

Popular posts from this blog

PRESS STATEMENT BY THE NATIONAL ASSOCIATION OF NIGERIAN STUDENTS (NANS)

Youthful and Dynamic Interior Minister Olubunmi Tunji-Ojo Intervenes, Advocates Leniency for Abdulganiy Muhammad

AREWA YOUTH FOR LIBERTY (AYFL) Condemns DAPPMAN’s Actions, Declares Full Support for Dangote Refinery